Wani Bapalastine Ya yi Shahada a Hanun Sahayuna
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i4762-wani_bapalastine_ya_yi_shahada_a_hanun_sahayuna
Jami'an tsaron HKI sun bindiga wani Bapalastine har Lahira
(last modified 2018-08-22T11:28:13+00:00 )
May 04, 2016 17:47 UTC
  • Wani Bapalastine Ya yi Shahada a Hanun Sahayuna

Jami'an tsaron HKI sun bindiga wani Bapalastine har Lahira

Ma'aikatar kiyon Lafiyar Palastinu ta sanar da cewa a yau Laraba Ahmad bn Riyad Abdul-Aziz ya yi shahada a yayin wani farmaki da ya kaiwa Yahudawan sahawuna da motarsa a yammacin garin Ramull..dake gefen kogin Jodan, inda ya jikkata uku daga cikin su

Jami'an tsaron HKI sun bindige Bapalstine mai sekaru 36 a duniya a Sansanin Kalandiya dake arewacin Qudus.

Rahoton ya ce a yau din nan Dakarun HKI cikin motoci masu sulke da manyan tankokin yaki sun kai farmaki a yankuna daban-daban na zirin Gaza, lamarin da ya janyo rufe wasu ma'aikatu da shaguna na yankin.

A nasu bangare, kungiyoyin gwagwarmaya na Hamas da Jihadul-islam sun Ja kunan magabatan HKI kan ci gaba da kai hare-haren , inda suka ce tsananta kai hare-haren a zirin Gaza ba zai hana ci gaba da gwagwarmaya ba.

Ko baya ga haka su san cewa za su mayar da martani cikin kankanan lokaci masu zuwa.

Tun daga farkon watan Oktoban shekarar 2015 din da ta gabata, Al'ummar Palastinu ke gudanar da zanga-zanga domin nuna Adawa da bakar siyasar magabatan HKI na mamaya inda suke rushe gidaje Palastinawa da nufin fadada Haramcecciyar kasar.