Ana ci gaba da kame Palastinawa daga Dakarun tsaron HKI
Dakarun tsaron Haramcecciyar kasar Isra'ila na ci gaba da kame Palastinawa da nufin hana Gwagwarmaya da Intifada ta Qudus
A jijjifin safiyar Yau Alkhamis Dakarun tsaron HKI sun kai farmaki kan gidajen Palastinawa a gariruwan Ramall...,Alkhalil da Bitulaham dake gabar tekun Jodan tare da yin awan gawa da mutane 12.
A Jiya Laraba ma Dakarun tsaron HKI sun yi awan gaba da Palastinawa 44 na yankuna daban-daban na kasar, daga farkon fara Intifadar Qudus a farkon watan Oktobar shekarar 2015 zuwa yanzu sama da Palastinawa dubu biyu ne aka tsare yayi wasu 215 suka yi shahada a hanun Dakarun tsaron na HKI.
A Daren jiya Laraba zuwa wayewar yau Alkhamis Jiragen yakin HKI sun yi lugudar wuta a yankuna daban daban na Palastinu, lamarin da ya yi sanadiyar Shahadar kananen yara uku da kuma jikkatar wani dattijo guda.