Akbar Wilayati Ya Fara Ziyara A Birnin Damascuss
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i4846-akbar_wilayati_ya_fara_ziyara_a_birnin_damascuss
Mai baiwa jagoran juyin musulunci na Iran shawara akan harkokin siyasa, Ali Akbar Wilayati ya fara ziyarar aiki a Kasar syria.
(last modified 2018-08-22T06:58:14+00:00 )
May 06, 2016 14:21 UTC
  • Akbar Wilayati Ya Fara Ziyara A Birnin Damascuss

Mai baiwa jagoran juyin musulunci na Iran shawara akan harkokin siyasa, Ali Akbar Wilayati ya fara ziyarar aiki a Kasar syria.

Kamfanin Dillancin Labarun Irna ya ce; Ali Akbar Wilayati wanda ya halarci taron malaman addinin musulunci masu goyon bayan gwagwarmaya a birnin Beirut na kasar Lebanon, ya isa birnin Damascuss a yau juma'a.

A jiya alhamis ne dai Akabar Wilayati ya gana da babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasarallah.

Bangarorin biyu dai sun tattauna halin da ake ciki ta fuskar siyasa a yankin gabas ta tsakiya.

A birnin Damascuss, Wilayati zai gana da jami'an gwamnatin Syria.