Shugaban Hukumar Palasdinawa Yana Gudanar Da Ziyarar Aiki A Kasar Masar
Shugaban Hukumar Cin Kwarya-Kwaryar Gashin Kan Palasdinawa yana gudanar da ziyarar aiki a kasar Masar domin tattauna hanyoyin kalubalantar bakar siyasar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila kan al'ummar Palasdinu.
A ganawarsa da Samaha Shukri ministan harkokin wajen kasar Masar a yammacin jiya Lahadi: Shugaban Hukumar Cin Kwarya-Kwaryar Cin Gashin Kan Palasdinawa Mahmud Abbas ya fayyace masa irin bakar siyasar da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila take ci gaba da gudanarwa a kan al'ummar Palasdinu musamman batun ci gaba da mamaye yankunan Palasdinawa da nufin aiwatar da gine-ginen matsugunan yahudawan sahayoniyya 'yan kaka gida.
A gefe guda kuma bangarorin biyu sun tattauna batun shirin zaman taron da za a gudanar a kasar Faransa kan daftarin kudurin da za a gabatar a gaban kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya da nufin neman hanyar shawo kan matsalar mamaye yankunan Palasdinawa da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke ci gaba da yi.
Zaman taron kasar ta Faransa dai zai fi mai da hankali ne kan neman hanyar wanzar da zaman lafiya da sulhu a tsakanin Hukumar Cin Gashin Kan Palasdinawa da mahukuntan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila 'yan mamaya.