Faransa Ta Yi Watsi Da Zargin Isra'ila Akan Falasdinu
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i5257-faransa_ta_yi_watsi_da_zargin_isra'ila_akan_falasdinu
Gwamnatin Faransa ta yi watsi da zargin da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi wa kasar na goyan bayan Falasdinawa akan shirin sasanta rikicinsu da Israila da take shiryawa.
(last modified 2018-08-22T06:58:16+00:00 )
May 16, 2016 06:37 UTC
  • Faransa Ta Yi Watsi Da Zargin Isra'ila Akan Falasdinu

Gwamnatin Faransa ta yi watsi da zargin da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi wa kasar na goyan bayan Falasdinawa akan shirin sasanta rikicinsu da Israila da take shiryawa.

Ministan harkokin wajen Faransa Jean Marc Ayrault ne ya yi watsi da furucin na Netanyahu wanda ke zargin cewar goyan bayan da Faransa ta bai wa hukumar UNESCO wadda ta amince da halascin Falasdinu, nuna kiyayya ce ga Israila.

Ayrault ya ce Faransa za ta ci gaba da taka rawa wajen ganin an samo masalaha kan takaddamar da ke tsakanin Yahudawa da Falasdinawa bayan ya gana da firaminista Benjamin Netanyahu da shugaba Mahmud Abbas.