Tsauraran Matakan Tsaro A Kasar Masar
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i532-tsauraran_matakan_tsaro_a_kasar_masar
Masar Ta Tsaurara Matakan Tsaro Akan Iyakokin Kasarta.
(last modified 2018-08-22T06:57:47+00:00 )
Feb 09, 2016 15:29 UTC
  • Tsauraran Matakan Tsaro A Kasar Masar

Masar Ta Tsaurara Matakan Tsaro Akan Iyakokin Kasarta.

Kamfanin Dillancin Labarun (AFP) ya ambato ministan tsaron kasar ta masar Sidqy Subhy yana jinjinawa manyan jami'an tsaron kasar da ke aiki a yankin al-garbiyyah, haka nan kuma kabilun da su ke kan iyakokin kasar saboda rawar da su ke takawa wajen tabbatar da tsaro.

Ministan tsaron kasar ta masar ya kuma ci gaba da cewa; Kasar tana da karfin da za ta iya tabbatar da tsaro duk da girman barazanar da ta ke fuskanta.

Har ila yau, ministan tsaron kasar ta Masar ya jinjinawa jami'an tsaron da su ka hada da 'yan sanda bisa kokarin da su ke yi na kare cibiyoyin gwamnati a cikin gida da kuma fuskantar 'yan ta'adda da masu karya dokoki.

Masar tan fuskantar matsalolin tsaro daga kungiyoyin su ke damfare da 'Da'esh, ( isil) a yankin Sina da ake kira; Ansaru Baitul-muqaddas.