Farmakin Dakarun Haramcecciyar kasar Isra'ila kan gidajen Palastinawa
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i5389-farmakin_dakarun_haramcecciyar_kasar_isra'ila_kan_gidajen_palastinawa
Sojojin Haramcecciyar kasar Isra'ila na ci gaba da kai farmaki kan gidajen Palastinawa tare da kame wani adadi daga cikinsu.
(last modified 2018-08-22T06:58:17+00:00 )
May 19, 2016 10:38 UTC
  • Farmakin Dakarun Haramcecciyar kasar Isra'ila kan gidajen Palastinawa

Sojojin Haramcecciyar kasar Isra'ila na ci gaba da kai farmaki kan gidajen Palastinawa tare da kame wani adadi daga cikinsu.

Kamfanin dillancin Labaran Wafa na yankin Palastinu ya habarta cewa A yau Alkhamis Dakarun tsaron Haramcecciyar kasar Isra'ila sun kai farmaki kan gidagen Palastinawa a gariruwan Tul-karam, Al-khalil da Janin dake gefen kogin Jodan tare da yin awan gaba da Palastinawa biyar.

Har ila yau Sojojin HKI sun yi awan gaba da wata Daliba Bafalastina a Baitul Makdis.

A jiya Laraba ma Dakarun tsaron na Haramcecciyar kasar Isra'ila sun yi awan da Palastinawa 19 daga cikin su har wasu daga cikin shugabanin Kungiyar gwagwarmaya ta Hamas a yankuna daban daban na gefeb tekun Jodan.

A bangaren guda tashar Telbijin din Al-aksa ta Palastinu ta habarta cewa Gwamnatin Mahmoud Abas ta jadadda daurin da take yiwa Tariq Abou Zaid Dan Jaridar tashar Telbijin din Al-Aksa na tsahon kwanaki 15.