Yan Gwagwarmayar Palasdinawa Sun Mai Da Martani Kan Zaluncin H.K.Isra'ila
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i5812-yan_gwagwarmayar_palasdinawa_sun_mai_da_martani_kan_zaluncin_h.k.isra'ila
Yan gwagwarmayar Palasdinawa sun kai harin mai da martani kan haramtacciyar kasar Isra'ila ta hanyar harba wasu makamai masu linzami kan matsugunan Yahaudawan Sahayoniyya 'yan kaka gida.
(last modified 2018-08-22T06:58:20+00:00 )
May 26, 2016 13:51 UTC
  • Yan Gwagwarmayar Palasdinawa Sun Mai Da Martani Kan Zaluncin H.K.Isra'ila

Yan gwagwarmayar Palasdinawa sun kai harin mai da martani kan haramtacciyar kasar Isra'ila ta hanyar harba wasu makamai masu linzami kan matsugunan Yahaudawan Sahayoniyya 'yan kaka gida.

Yan gwagwarmayar Palasdinawa sun harba makamai masu linzami daga yankin Zirin Gaza kan matsugunan Yahudawan Sahayoniyya 'yan kaka gida da suke kudancin yankin Palasdinu da aka mamaye a yau Alhamis.

Yan gwagwarmayar Palasdinawan sun jaddada cewa; Al'ummar Palasdinu ba zata taba zama haka kawai suna zuba ido sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suna kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kansu ba tare da mai da martani ba, don haka suna nan a kan bakansu na ci gaba da gwagwarmaya da bakin zaluncin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila.

Har ila yau dakarun bangaren sojin Izzuddeen Qassam da ke karkashin kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas sun kai farmaki da manyan makamai kan wasu jiragen saman yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila da suke shawagi a yammacin yankin Zirin Gaza a yau Alhamis lamarin da ya tilastawa jiragen tserewa.