Masar: An kashe Sojojin Gwamnati Shida.
Jun 01, 2016 03:30 UTC
Wani Bom da ya tashi a masar ya ci rayukan sojoji 6.
Kamfanin Dillancin Labarun Associated Press ya ambato majiyar tsaron Masar na fadin cewa; Sojojin kasar shida sun kwanta dama sanadiyyar tashin wani bom a bakin hanyar da motarsu ta ke wucewa a gundumar Sina ta arewa.
Kwanaki biyu da su ka gabata ne dai sojojin kasar ta Masar su ka sanar da kai farmaki a yankin wanda ya yi sanadin kashe masu dauke da makamai 36.
Sanarwar ta kunshi cewa; sojojin su kuma yin nasarar lalata bama-bamai 24 da 'yan ta'addar su ka dasa. Bugu da kari sojan na Masar sun rushe gidaje 19 da maboya 16 da 'yan ta'addar su ke amfani da su.
Kawo ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin.
Tags