Nuna Goyon Bayan Al’ummar Bahrain Ga Sheikh Ali Salman
Al’ummar kasar Bahrain na nuna goyon bayanta ga babban sakataren jam’iyyar Al-wifaq sheikh Ali Salman tare da yin kira da a sake shi.
Tashar talabijin ta Press TV ta bayar da rahoton cewa, Jama'a da dama ne suka fito kan tituna a yankuna daban-daban na Bahrain a jiya Juma'a, suna jerin gwano na nuna goyon bayansu ga babban sakataren jam’iyyar wifaq sheikh Ali Salman wanda ake tsare da shi tare da daruruwan fursunonin siyasa.
Masu jerin gwanon sun bayyana tsare Sheikh Salman da ake yi a matsayin wani nau'i na zalunci da danne hakkokin bil adama da masarautar mulkin mulukiyya ta kasar take yi a kan 'yan siyasa da masu fafutuka daga cikin al'ummar kasar.
Tun a ranar 28 ga watan Disamban shekara ta 2014 ce dai mahukuntan kasar ta Bahrain suka kame sheikh Ali Salman da sunan cewa za su yi bincike akansa, amma daga bisani sai suka sanar da yanke masa hukuncin daurin shekaru hudu a gidan kaso a cikin shekara ta 2015, amma kuma daga bisa a ranar 30 ga watan Mayun da ya gabata, kotun masarautar mulkin mulukiya ta kasar Bahrain ta sanar da cewa, ta kara tsawon shekarun daure sheikh Salman daga shekaru 4 zuwa 9 a gidan kaso.
Kama sheikh Ali Salman dai ya fuskanci kakkausar suka daga kasashen duniya, da kuma kungiyoyin kare hakkin bil adama na duniya.