Harin 'Yan Sahayoniya A Yammacin Kogin Jordan
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i6589-harin_'yan_sahayoniya_a_yammacin_kogin_jordan
Sojojin Sun Kai Farmaki A Kauyen Bani Na'im da ke yammacin Kogin Jordan.
(last modified 2018-08-22T11:28:25+00:00 )
Jun 11, 2016 18:53 UTC
  • Harin 'Yan Sahayoniya A Yammacin Kogin Jordan

Sojojin Sun Kai Farmaki A Kauyen Bani Na'im da ke yammacin Kogin Jordan.

Kamfanin Dillancin labarun "Wafa" na gwamnatin Palasdinu ya ambato majiyar tsaro palasdinu na cewa; Sojojin yahudawan Sahayoniya sun kai farmaki a garin "Bani Na'im" da ke gundumar Khalil tare da gudanar da bincike cikin gidaje.

 

Majiyar ta ci gaba da cewa sojojin na 'yan sahayoniya sun lalata kayan gidajen da su ke rika shiga, kamar kuma yadda su ka rusa wata cibiyar bincike ta kiwon lafiya da Khalil.

 

Babu kwakkwaran dalili da ya sa sojojin yahudawan su ka kai farmaki a cikin wannan yankin.