Shugaban Palasdinawa Ya gargadin "Yan Sahayoniya Akan Masallacin Qudus.
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i6652-shugaban_palasdinawa_ya_gargadin_yan_sahayoniya_akan_masallacin_qudus.
Abbas Abu Mazin: Masallacin Qudus Jan Layi Ne A Wurinmu:
(last modified 2018-08-22T06:58:26+00:00 )
Jun 13, 2016 03:49 UTC
  • Shugaban Palasdinawa  Ya gargadin

Abbas Abu Mazin: Masallacin Qudus Jan Layi Ne A Wurinmu:

Kamfanin Dillancin Labarun Palasdinu ya nakalto shugaban gwamnatin Palasdinawa Mahmud Abbas Abu-Mazin yana cewa; Masallacin Qudus wani jan layi ne a wurinmu, ba za mu bari a wulakanta shi ba.

Abbas Abu Mazin wanda ya gana da masu kula da masallacin na Qudus da 'yan Sahayoniya su ka kora, ya jaddada muhimmancin tsayin daka domin fuskantar 'yan sahayoniya.

Shugaban na Palasdinawa ya kuma ce; Al'ummar Palasdinu za su kare masallacin Qudus da kuma duk wurare masu tsarki da su ke da shi.

Haramtacciyar Kasar Isra'ila dai ta sha barin 'yan share wuri zauna na yin kutse cikin masallacin wanda hakan ya ke a matsayin share fage na raba masallacin gida biyu, da bai wa Palasdianwa rabinsa.