Bahrain: An Kame Wani Kusa Na kare Hakkin Bil'adama.
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i6655-bahrain_an_kame_wani_kusa_na_kare_hakkin_bil'adama.
Sojojin kasar Bahrain sun kame Nabil Rajab Na Kungiyar Kare Hakkokin Bil'adama.
(last modified 2018-08-22T11:28:26+00:00 )
Jun 13, 2016 08:20 UTC
  • Bahrain: An Kame Wani Kusa  Na kare Hakkin Bil'adama.

Sojojin kasar Bahrain sun kame Nabil Rajab Na Kungiyar Kare Hakkokin Bil'adama.

Mai dakin mutumin da aka kame, Sumayyah Rajab, ta buga a shafinta na Internet cewa; Sojojin sun shiga sun kan karai, kuma sun yi awon gaba da mai dakinta.

Shi dai Nabil Rajabi yana daga cikin kusoshin jam'iyyun hamayyar kasar, wanda a baya ma dai an sha kamashi.

Makwanni biyu da su ka gabata mahukunta a kasar ta Bahrain sun daure Sheikh Ali Salman zaman kurkuku na shekaru 8.

Shekaru kusan 5 kenan da al'ummar kasar su ka yunkura da zummar kawo sauye-sauyen siyasa a cikin kasar, sai dai mahukunta sun yi amfani da karfi wajen murkushe su.