Babban Sakataren Kungiyar Kasashen Larabawa Ya Jinkirta ziyararsa Zuwa Palastinu
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i6715-babban_sakataren_kungiyar_kasashen_larabawa_ya_jinkirta_ziyararsa_zuwa_palastinu
Israela ta hana tafiyar Nabil Al-Arabi zuwa Palasdinu har sau biyu
(last modified 2018-08-22T06:58:26+00:00 )
Jun 14, 2016 06:41 UTC
  • Babban Sakataren Kungiyar Kasashen Larabawa Ya Jinkirta ziyararsa Zuwa Palastinu

Israela ta hana tafiyar Nabil Al-Arabi zuwa Palasdinu har sau biyu

Babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa Nabil Al-Arabi ya sake daga tafiyarsa zuwa Palasdinu don ganawa da shugaba Mahmood Abbas. Kamfanin dillancin labaran Chinhuwa na kasar China ya bayyana cewa da farko an jirkirta tafiyan ne zuwa yau Talata sannan daga baya aka sake daga shi zuwa wani lokacinda da ba'a bayyana na ba.

Wata majiyar gwamnatin yamma da kogin Jordan ta bayyana cewa dalilin jinkirin tafiyar rashin samun amincewar Haramtacciyar kasar Israela ne. Al-Arabi ya bukaci ziyartar yamma da kogin Jordan ne don tattaunawa tare da jami'an gwamnatin Palasdinawa kan Matsalolin da yankin yake fama da shi na tashe tashen hankula.