Masarautar Bahrain Ta Haramta Babbar Jam'iyyar Siyasa A Kasar
Masarautar mulkin mulukiya ta kasar Bahrain ta haramta jam'iyyar Alwifaq jam'iyyar siyasa mafi girma a kasar, da nufin kawo karshen duk wani bangare da ke adawa da salon siyasar mulkin mulukiya na kasar da bai yi imani da dimukradiyya ba.
Tashar talabijin ta Press TV ta bayar da rahoton cewa, kotun masarautar kasar ta Bahrain ce ta bayar da bayar da umarni ga jami'an 'yan sanda da suka kai farmaki kan babban ofishin jam'iyyar da ke birnin Manama ba tare da sanar da 'ya'yan jam'iyyar ba ko kuma ba su notis, inda 'yan sandan masarautar ta Bahrain suka afka kan ofishin tare da cin zarafin jama'a da ke wurin, kwashe kaddarorin jam'iyyar, tare da garkame ofishin.
Wannan mataki dai ya fuskanci kakkausar suka daga bangarori daban-daban na duniya, da hakan ya hada da majalisar dinkin duniya da kuma wasu daga cikin kasashen turai, musamamn gwamnatin kasar Switzerland, wanda ta bayyana hakan a matsayin wani aiki na cin zarafin 'yan adam da kuma yi musu mulkin kama karya.
Kafin wannan lokacin dai mahukuntan kasar sun kame babban sakataren jam'iyyar ta Alwifaq Sheikh Ali salman, tare da yanke masa hukuncin daurin shekaru hudu a gidan kaso, kafin daga bisani kuma suka mayar da hukuncin daurin shekaru tara a gidan kaso, kamar a ranar Litinin da ta gabata mahukuntan Bahrain suka kame Nabil Rajab shugaban cibiyar kare hakkin bil adama ta kasar ba tare da wani dalili ba.