Masar An Shigar Da Sunayen "Yan'uwa Musulmi Cikin Jerin 'yan ta'adda
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i6781-masar_an_shigar_da_sunayen_yan'uwa_musulmi_cikin_jerin_'yan_ta'adda
A kalla Sunayen mutane 215 na Kungiyar Ikhwanul-Muslimin Wata Kotu ta shigar cikin na 'yan ta'adda.
(last modified 2018-08-22T06:58:27+00:00 )
Jun 15, 2016 14:35 UTC
  • Masar An Shigar Da Sunayen

A kalla Sunayen mutane 215 na Kungiyar Ikhwanul-Muslimin Wata Kotu ta shigar cikin na 'yan ta'adda.

An ci gaba da shigar da sunayen 'yan kungiyar Ikhwanul-Muslimin a cikin jerin 'yan ta'adda a kasar Masar.

Kamfanin Dillancin Labarun Tasnim ya nakalto jaridar "alwaqa'iul-Misriyyah" da wata kotu ta bijiro da sunayen 'yan kungiyar Ikhwanul-muslimin 215 a cikin jerin sunayen 'yan ta'adda.

Jaridar ta ci gaba da cewa hukuncin wanda aka fitar da shi a cikin watan Aprilu kuma ya zama wanda ake aiki da shi, zai ci gaba har nan da shekaru uku masu zuwa.

A gefe daya, Lauyan da ke jagorantar kare 'yan 'uwa musulmi, Abdulmunim Abdulmaqsud, ya bayyana mamakinsa akan fitar da wannan hukuncin, sannan kuma ya ce; Za su kalubalancin hukunci a kotu.

A shekarar 2013 ne dai gwamnatin kasar ta Masar ta bayyana kungiyar 'yan'uwa musulmi a matsayin kungiyar 'yan ta'adda.

Tun bayan faduwar gwamnatin Muhammadu Mursi, ne ake ci gaba da kama da kuma hukunta magoya bayansa a karkashin laifukan da su ka kunshi ta'addanci da hargitsa zaman lafiya.