Masarautar Bahrain Na Cin Zarafin Manyan Malaman Addini A Kasar
A wani mataki na kara ruruta wutar bangaranci na mazhabanci a kasar Bahrain, masarautar mulkin mulukiya ta kasar tana kara tsananta matakan da take dauka na cin zarafin malamai da kuma manyan siyasa mabiya mazhabar shi'a a kasar.
A cikin wannan makon ne kotun masarautar Bahrain ta sanar da haramta jam'iyyar Alwifaq, jam'iyyar siyasa mafi girma a cikin dukkanin kasashenlarabawa na yankin tekun fasha, wadda fiye da rabin mutanen kasar ta Bahrain suke goyon bayanta, inda jami'an tsaro a cikin kayan sarki suka kaddamar da farmaki a kan babban ofishin jam'iyyar da ke Manana fadar mulkin kasar, suka ci zarafin dukkanin mutanen da suka samu a wurin, suka kuma sace muhimman kaddarori na jam'iyyar da suke a cikin ofishin, kafin daga bisani kuma suka rufe wurin baki daya suka tafi da makullan.
Kafin daukar wannan mataki da 'yan kwanaki, kotun masarautar ta kara tsawon wa'adin daurin da ta yi wa babban sakataren jam'iyyar Sheikh Ali Salman, inda a baya ta sanar da daure shi shekaru hudu a gidan kaso, amma a cikin 'yan kwanakin da suka gabata ta sanar da mayar da hukuncin zuwa daurin shekaru 9 a gidan kaso, bisa zarginsa da yin kalamai na sukar salon siyasar wannan masarauta.
A cikin kasa da sa'oi arba'in da takwas da suka gabata, jami'an tsaron masarautar Bahrain sun kira yi manyan malaman addini da limaman Juma'a na mabiya mazhabar shi'a a kasar, inda suka ja kunnensu dangane da gudanar da salla ko sauran ayyuka na ibada sabanin mahangar masarautar, tare da hana su yin magana a kan dukkanin abin da ya shafi batu na siyasa ko salon mulki a kasar.
Kimanin kashi 86% na al'ummar kasar Bahrain dai mabiya mazhabar shi'a ne, amma kuma masarautar da ke mulki a kasar wadda 'yan mulkin mallaka na Birtaniya suka kafa iyalan gidan Khalifa ne, wadanda 'yan sunna ne, kuma tun kimanin shekaru hamshin da suka gabata su ne suke mulki a kasar, to amma daga bisani sakamakon tasirin wasu manyan kasashen larabawan yankin tekun fasha a kan wanann masarauta, ta fara nuna banbanci na mazhabar a tsakanin al'ummar kasar, musamman ma a kan mabiya mazhabar shi'a, wadanda su ne akasarin al'ummar kasar.
A cikin yan shekarun baya-bayan nan masarautar bahrain ta tashi ka'in da na'in wajen ganin da murkushe yunkurin da al'ummar kasar suka yi na neman a samar da tsari na dimukradiyya a karkashin tsarin sarautar kasar, inda sarki zai ci gab da mulkinsa, amma a gefe guda a kafa majalisar dokoki wadda 'yan kasa za su zabi mambobinta da kansu, tare da rubuta kundin tsarin mulki, da kuma kafa majalisar ministoci a karkashin Firayi minista wanda majalisa za ta zaba.
Wannan kira na al'umma suka ya jawo fushin masarautar kasar, inda yanzu haka akwai mutane fiye da dubu daya da suke tsare ana azabtar da su, da suka hada da manyan 'yan siyasa da kuma masu fafutukar kare hakkokin bil adama, yayin da wasu kuma aka kashe wasu daruruwa ta hanyar azabtarwa a cikin gidajen kaso na wannan masarauta, kamar yadda kuma a kori wasu daruruwa daga kasar wadanda 'yan asalin kasar ne, ala tilas suka yi hijira zuwa wasu kasashe, haka nan kuma masarautar tana ci gaba da kwaso mutane daga kasashen Jordan da Pakistan da wasu kasashen larabawa tana mayar da su 'yan kasa, domin adadin masu goyon bayan masarautar ya karu, inda a halin yanzu hatta manyan jami'an tsaron kasar 'ya Jordan ne da Pakistan, duk da nufin kara dankwafe 'yan asalin kasar wadanda mabiya mazhabar shi'a ne.
To sai dai a wannan karon wasu daga cikin manyan kasashen duniya da kuma majalisar dinkin duniya sun fara sanya baki a cikin lamarin, inda suke ganin cewa an kama hanyar kama karya babu kama hannun yaro a kasar, inda kuma suke yin kira ga masarautar mulkin mulukiya ta kasar Bahrain da ta gaggauta sakin malamai da kuma 'yan siyasa da take tsare da su saboda dalilai na banbancin mazhaba da siyasa.