Gangamin Al'ummar Bahrain A Garin Diraz Mahaifar Sheikh Isa Qasim
-
Al'ummar Bahrain A Garin Diraz Mahaifar Sheikh Isa Qasim
Mutanen kasar Bahrain suna ci gaba da yin zaman dirshan a a cikin garin Diraz na kasar Bahrain, domin kare rayuwar babban malami a kasar bisa barazanar da yake fuskanta daga masarautar mulkin mulukiya ta kasar.
Kamfanin dillancin labaran Fars ya bayar da rahoton cewa, tun bayan da masarautar Bahrain ta sanar da janye shedar zama dan kasa a kan babban malami mafi karfin fada a ji a kasar Ayatollah Sheikh Isa Ahmad Kasim, saboda dalilai na siyasa da banbancin mazhaba, al'umma a ko'ina cikin fadain kasar suna nuna fushinsu dangane da wannan mataki.
Kamar yadda a garin Diraz mahaifar shehim malamin inda kuma a nan yake rayuwa, dubban mutane sun fito a ko'ina yayin da wasu kuma suke zaman dirshan a kofar gidansa, inda suka sha alwashin cewa sai dai a bayan ransu ne mahukuntan kasar za su iya taba shi.
Rahoton ya ce a ko'ina cikin kasar mutane na cikin shirin fuskantar kowane irin mataki da masarautar ka iya dauka a kan malamin, lamarin da ake ganin zai iya jefa kasar cikin wani rikici da bata taba ganin irinsa ba.
A nata bangaren masarautar Saudiyya ta fito ta yi na'am da wannan mataki, inda ta bayyana cewa an yi hakan ne domin kawo karshen sukar mahukunta da malamin yake yi kan salon mulki a kasar, kuma hakan a cewar majalisar malaman Saudiyya bai saba ma shari'a ba.
A nasa bangaren mai magana da yawun ofishin Ayatollah sheikh isa Kasim Sheikh Abdullah Daqqaq ya fadi a yau Talata cewa, suna cikakken bayani a kan cewa gwamnatin Saudiyya ce ta umarci masarautar Bahrain da ta yi hakan, domin ya zama daukar fansa kan kisan dubban 'yan ta'addan ISIS da sojojin Iraki suka yi Falluja, tare da kwace birnin daga 'yan ta'addan, wanda gwamnatin Saudiyya ita kadai ce kasar da a hukumance ta yi kakkausar suka da Allawadai da wannan nasara da sojojin Iraki suka samu a kan 'yan ta'addan takfiriyyah Wahabiyyah na ISIS.