Tattaunawar Ayatollah Sistani Tare Da Ayatollah Isa Kasim Ta Wayar Tarho
Babban malamin addini na kasar Iraki Ayatollah Sayyid Ali Sistani ya tuntubi babban malamin addini na kasar Bahrain Ayatollah Sheikh Isa Kasim ta wayar tarho, domin kara tabbatar da cikakken goyon baya gare shi a kan zaluncin da yake fuskanta daga 'yan mulkin mulukiya a kasar.
Tashar talabijin ta Alalam ta bayar da rahoton cewa, a tattaunawar da ta gudana a tsakanin manyan malaman biyu, Ayatollah Sistani ya jinjina wa Ayatollah Isa Kasim, dangane da namijin kokarin da yake yi wajen kare hakkokin al'ummar kasar Bahrain a matsayin sa na uba kuma malami gare su, tare da yin amfani da hanyoyi na hikima da ilimin da Allah ya ba shi.
Haka nan kuma Ayatollah Sistani ya sheda ma Ayatollah Isa Kasim da cewa, zai yi iyakacin kokarinsa domin tabbatar da cewa an kare dukkanin hakkokinsa a matsayinsa na dan kasa na asali a Bahrain.
Mahukuntan kasar Bahrain wadanda ke bin akidar wahabiyanci, wadanda kuma su ne 'yan tsiraru a kasar, tare da taimakon masarautar Saudiyya sun tsananta cin zarafi da kuma muzgunawar da suke yi wa mabiya mazhabar shi'a wadanda su ne masu gagarumin rinjaye a kasar, saboda dalilai na siyasa da bangarancin mazhaba.