Dauki Ba Dadi Tsakanin Masallata Da Yahudawa A Cikin Masallacin Quds
A jiya an yini a na dauki ba dadi tsakanin masallata musulmi da kuma yahudawan sahyuniya a cikin masallacin Qods mai alfarma.
Kamfanin dilalncin labaran Ma'an na Palastinu ya bayar da rahoton cewa, daruruwan yahudawa 'yan share wuri zauna ne suka kaddamar da farmaki a kan musulmi masallata a cikin masallacin Qouds mai alfarma a jiya da rana tsaka, tare da daruruwan jami'an 'yan sandan Isra'ila masu mara musu baya.
Sheikh Umar Kusul shi ne mai kula da dukkanin harkokin da suka shafi masallacin Quds, ya bayyana cewa yahudawan sun kawo farmakin ne domin tsokana, kuma ga dukaknin alamu an riga an shirya hakan ne domin neman haifar da wata fitina, ta yadda Isra'ila za ta samu damar hana gudanar da gangamin ranar Quds ta duniya a ranar Juma'a mai zuwa.
Shi ma a nasa bangaren Sheikh Azzam Khatib babban malami mai kula da ayyukan babbar cibiyar addinin muslunci ta birnin Quds ya bayyana cewa, yahudawan sun kai wannan farmaki ne akan masallata da musulmi masu gudar da i'itikafi a cikin wannan masallaci domin tsokanar musulmi.
Musulmin da ke cikin masallacin dai sun hana yahudawa shiga cikin dakin masallacin, yayin da jami'an 'yan sandan Isra'ila suka yi ta antaya hayaki mai sanya hawaye a cikin haraba da kuma ginin masallacin mai alfarma, inda suka jikkata masallata kimanin 24.