An halaka wani bayahude guda a gabar kogin Jodan.
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i7459-an_halaka_wani_bayahude_guda_a_gabar_kogin_jodan.
A ci gaba da kai harin kare kai, Palastinawa sun hallaka wani Bayahude guda
(last modified 2018-08-22T11:28:31+00:00 )
Jun 30, 2016 11:15 UTC
  • An halaka wani bayahude guda a gabar kogin Jodan.

A ci gaba da kai harin kare kai, Palastinawa sun hallaka wani Bayahude guda

Tashar telbijin ta Al-Alam dake watsa shiriye-shiryenta daga nan birnin Tehran ta habarta cewa a wannan Alkhamis wani Balastine ya hallaka wani Bayuhude tare da jikkata wani na daban a garin Kariyatu Arba'a dake kusa da Alkhali na gabar tekun Jodan, wannan kuwa na zuwa ne a matsayin mayar da martani kan ta'addancin da Sojojin HKI ke aikatawa kan Al'ummar ta Palastinu.

A bangare guda Dakarun HKI sun kashe wani matashin Balastine tare da jikkata wasu biyu na daban a kusa da garin Khalil dake gabar tekun Jodan.

Daga farkon watan Oktoban shekarar 2015 zuwa yanzu yankuna daban daban na Yankin Palastinu na ci gaba da bayyana adarsu na hare-haren wuce gona da iri daga magabatan birnin Tel-Aviv ke kaiwa a kansu da kuma kokarinsu na canza yanayin Baitul-Makdis gami da raba Masallacin Al-Aksa.

Ta'addancin na Magabatan HKI ya sanya Palastinawan shelantar Intifar Qudus, daga kuma wancan lokacin zuwa yanzu Akalla Yahudawa 35 ne suka hallaka.