Masar: An shigar da Sunan Mursi A cikin Jerin 'yan ta'adda.
Ma'aikatar Shari'ar Kasar Masar ta shigar da sunan tsohon shugaban kasar a cikin sunayen 'yan ta'adda.
Jaridar gwamnatin Masar ta al-waqa'ie, fitowar jiya litinin ta ce; Ma'aikatar shari'ar kasar ta Masar ta shigar da sunan Muhammadu Mursi a cikin jerin sunayen 'yan ta'adda ne tun a cikin watan Aprilu.
Bugu da kari da akwai sunayen wasu mutanen 35 da aka shigar cikin jerin sunayen 'yan'ta'addar da dukkaninsu 'yan kungiya rne ta Ikhwanul-muslimin.
Lauya mai kare 'yan kungiyar ta Ikhwan 35, Isma'ila Abu Barkah, da ya ke tsokaci akan fitar da bayanin kotun a jiya litinin, ya ce; Ba a sanar da shi akan matakin da aka dauka ba tun a cikin wata Aprilu.
A ranar 16 ga watan Yuli ne dai kotun ta yanke hukuncin zaman kurkuku na har abada ga tsohon shugaban kasar ta Masar Muhammadu Mursi da kuma shugaban kungiyar 'yan 'uwa musulmi, Muhammad Bade'i.