Palasdinu
Majalisar Dinkin Duniya Ta ce: "Za A Ci Gaba Da Rikici A Gabas Ta Tsakiya Idan Ba a Kafa Gwamnatin Palasdinawa ba.
Kamfanin Dillancin Labarun Reuters ya ambato wani babban jmai'in majalisar dinkin duniya a gabas ta tsakiya yana cewa; Da alama batun kafa gwamnatin Palasdinu ya sake samun koma baya fiye da kowane lokaci, kuma matukar wadanda lamarin ya shafa ba su yi wani abu ba, to da akwai hatsarin barkewar rikici mai tsanani anan gaba.
Manzon Musamman na Majalisar Dinkin Duniya a gabas ta tsakiya, Nicolay Maladinov, ya ce; Al'ammurra sun kusa isa magaryar tukewa.
Maladinov ya yi ishara da gina matsugunan yahudawa 'yan share wuri zauna, da kuma abinda ya kira; hare-haren da Palasdinawa su ke kai wa, a matsayin abubuwan da su ke kawo cikas.
Bugu da kari, manzon musamman na Majalisar Dinkin Duniyar ya kara da cewa; "Watakila batun kafa kasashe biyu ya sake samun koma baya matuka fiye da kowane lokaci a baya."
Gargadin na Maladinov dai ya zo ne kwanaki kadan bayan rahoton da kwamati mai bangarori 4 ya fitar dangane da halin da ake ciki a gabas ta tsakiya.