Hukumar Cin Gashin Kan Palasdinu Ta Bukaci Kawo Karshen Kisan Palasdinawa
Ma'aikatar harkokin wajen hukumar cin kwarya-kwaryar gashin kan Palasdinawa ta bukaci kawo karshen hare-haren wuce gona da iri kan Palasdinawa.
A bayanin da ma'aikatar harkokin wajen hukumar cin gashin kan Palasdinawa ta fitar a jiya Litinin ta jaddada yin kira ga hukumomin kasa da kasa gami da gwamnatocin kasashen duniya kan hada karfi da karfe da nufin daukan matakin matsin lamba kan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila domin kawo karshen kashe -kashen gillar da take yi kan al'ummar Palasdinu tare da rushe -rushen gidajen Palasdinawa.
A gefe guda kuma sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun kai harin wuce gona da iri kan sansanin 'yan gudun hijira na Al-Urub da ke yankin garin Khalil a gabar yammacin kogin Jordan a jiya Litinin, inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi lamarin da ya kai ga shahadar bafalasdine guda.