Shugaban Kasar Masar Ya Bayyana Aniyarsa Ta Warware Matsalar Palasdinu
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i8515-shugaban_kasar_masar_ya_bayyana_aniyarsa_ta_warware_matsalar_palasdinu
Shugaban kasar Masar ya bayyana aniyarsa ta dukufa a fagen ganin ya warware matsalar al'ummar Palasdinu.
(last modified 2018-08-22T06:58:38+00:00 )
Jul 23, 2016 01:20 UTC
  • Shugaban Kasar Masar Ya Bayyana Aniyarsa Ta Warware Matsalar Palasdinu

Shugaban kasar Masar ya bayyana aniyarsa ta dukufa a fagen ganin ya warware matsalar al'ummar Palasdinu.

A jawabinsa a taron bikin yaye sabbin dalibai a jami'ar soji ta Masar a jiya Juma'a: Shugaban kasar Abdul-Fatah Al-Sisi ya yi furuci da cewa: Gwamnatinsa zata yi iyaka kokarinta na ganin ta warware matsalar Palasdinu tare da jaddada yin kira ga dukkanin bangarorin da abin ya shafa na ganin sun yi aiki da hakkin da ya rataya a wuyarsu.

Al-Sisi ya yi furuci da cewa: Matsalar Palasdinu ita ce babbar matsalar da tafi dukkanin matsalolin da suke ci gaba da addabar yankin gabas ta tsakiya, sakamakon haka ya zame dole a dauki matakin ganin an samu wanzar da zaman lafiya da sulhu a dukkanin yankin.

Kwanaki 10 da suka gabata shugaban kasar ta Masar ya tura ministan harkokin wajen kasarsa Samaha Shukri zuwa haramtacciyar kasar Isra'ila domin ganawa da fira ministan gwamnatin yahudawan sahayoniyya Benyamin Natenyahu da nufin neman hanyar farfado da zaman tattaunawa tsakanin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila da Hukumar cin gashin kan Palasdinawa.