Tawagar Jami'an Saudiyyah A Haramtacciyar Kasar Isra'ila
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i8560-tawagar_jami'an_saudiyyah_a_haramtacciyar_kasar_isra'ila
A cikin wannan mako ne wata tawagar kasar Saudiyyah karkashin jagorancin Anwar Ishki, wani tsohon janar na sojin sojin Saudiyya, kuma tsohon shugaban bangaren ayyukan leken asiri na soji a kasar, wanda ke jagorantar wata cibiyar bincike kan harkokin tsaro a halin yanzu a birnin Jidda.
(last modified 2018-08-22T11:28:38+00:00 )
Jul 24, 2016 08:19 UTC
  • Tawagar Jami'an Saudiyyah A Haramtacciyar Kasar Isra'ila

A cikin wannan mako ne wata tawagar kasar Saudiyyah karkashin jagorancin Anwar Ishki, wani tsohon janar na sojin sojin Saudiyya, kuma tsohon shugaban bangaren ayyukan leken asiri na soji a kasar, wanda ke jagorantar wata cibiyar bincike kan harkokin tsaro a halin yanzu a birnin Jidda.

Jaridar Haaretz ta Isra'ila ta ce wannan tawaga ta Saudiyya ta gana da wasu manyan jami'an Isra'ila a Tel Aviv, da suka hada da babban daraktan ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila Dori Golod, da kuma wasu daga cikin 'yan majalisar dokoki ta Kneset.

Jagoran tawagar ta Saudiyyah a Isra'ila Anwar Ishki, ya sheda ma labarai cewa shi ne masarautar Saudiyyah ta kallafa wa aikin kyautata alaka a tsakaninta da Isra'ila, duk kuwa da cewa wasu kafofin yada labarai na yahudawan sahyuniya sun ce wannan ba shi ne karon farko da Anwar Ishki yake zuwa Isra'ila tare da ganawa da jami'anta ba, amma dai wannan shi ne karon farko da aka sanar da ziyarar a hukumance daga bangaren Isra'ila da kuma Saudiyyah.

Babbar manufar wannan kawance a tsakanin Isra'ila da Saudiyyah ba wani abu ba ne illa yaki da wadanda suke kira makiyansu na bai daya a yankin gabas ta tsakiya, wato Iran, Hizbullah da kuma gwamnatin Syria, kamar yadda firayi ministan haramtacciyar kasar ta Isra'ila Benjamin Netanyahu ya sha nanatawa cewa, Isra'ila tana aiki ne tare da manyan kasashen larabawa wajen aiwatar da dukkanin manufofin da suka yi tarayya a kansu, wato dakushe karfin Iran a yankin gabas ta tsakiya baki daya.

Wannan kawance na Saudiyyah da Isra'ila na da nufin hada alaka a tsakanin kasashen larabawa da Isra'ila ne a hukumance, duk kuwa da cewa akasarin kasashen larabawa dama suna da kyakkyawar alaka da Isra'ila, ko dai a bayyane ko kuma a karkashin kasa.

Batun kawo karshen cin zalun da kisan kiyashin da Isra'ila take yi a kullum rana a kan larabawan Palastinu, da kuma daina keta alfarmar wurare masu tsarki da yahudawan Isra'ila ke yi suka hada da masallacin Quds, dawo da miliyoyin palastinawa da Isra'ila ta mayar da su 'yan gudun hijira a kasashe daban-daban, da kafa kasar Palastinu mai cin gishin kanta a kan iyakokin palastinu na shekara ta 1967, da kawo karshen mamaye yankunan palastinawa da rusa musu gidaje da wuraren noma, duk wannan baya daga cikin ajandar larabawa a hankoron da suke yi na kara kyautata alakarsu da Isra'ila a hukumance.

Ziyarar tawagar saudiyyah a Isra'ila a cikin wannan mako tana dauke da sakonni na siyasa daban-daban, mafi muhimamnci daga ciki shi ne, amincewa da Isra'ila a hukumance kuma a bayyane daga bangaren Saudiyyah, ba tare da Isra'ila ta canja matsayinta a kan lamarin palastinawa ba, sako na biyu kuma shi ne, Benjamin Netanyahu ya kara tabbatar da karfin siyasarsa a cikin gida, domin kuwa ya mayar da gwamnatocin larabawa a bokan kawancesa ba tare da ya canja siyasarsa a kan 'yan uwansu palastinawa ba.