Shara'ar Shekh Isa na Kasar Bahrain
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i8710-shara'ar_shekh_isa_na_kasar_bahrain
Gwamnatin Kasar Bahrain ta ce a gobe Laraba ne za fara sauraren shara'ar Shekh Isa Kasim shugaban mabiya mazhabar shi'a na kasar
(last modified 2018-08-22T11:28:39+00:00 )
Jul 26, 2016 11:20 UTC
  • Shara'ar Shekh Isa na Kasar Bahrain

Gwamnatin Kasar Bahrain ta ce a gobe Laraba ne za fara sauraren shara'ar Shekh Isa Kasim shugaban mabiya mazhabar shi'a na kasar

Tashar telbijin din Almanar ta kasar Labanon ta habarta cewa a wannan talata Kotun hukunta manya laifuka ta kasar Bahrain ta sanar da fara sauraren karan Shugaban mabiya mazhabar shi'a na kasar Bahren Shekh Isa Kasim wanda ake zarki da laifin tunzura Al'umma wajen yiwa Gwamnati tawaye a gobe Laraba.

Kafin wannan sanarwa Al'ummar yankin Adderaz na birnin Manama sun taru a gaban kotun domin neman kotun da ta sanya ranar sauraren karar na shekh Isa Kasim.

Gwamnatin ta Bahrain na ci gaba da kamen manya-manyen malimai mabiya mazhabar Shi'a da kuma dukkanin wani Dan siyasa ko kuma babban mutun dake adawa da siyasar ta.

A bangare guda, kungiyoyin kasar dake adawa da bakar siyasar masarautar Ali khalifa dake zaune a kasashen waje sun bukaci kungiyoyin kasa da da kasa da kasashen masu 'yanci na Duniya da su dauki matakin gaggawa domin kawo goyon bayansu ga Al'ummar kasar Bahrain, inda suka Ayyana ranar juma'a 29 ga wannan wata na Yuli shekarar 2016 a matsayin  ranar goyon bayan Al'ummar kasar Bahrain.