Masarautar Bahrain Ta Kame Manyan Malamai Uku Na Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i9271-masarautar_bahrain_ta_kame_manyan_malamai_uku_na_kasar
Masarautar mulkin mulukiya ta kasar Bahrain ta kame manyan malaman addini na kasar guda uku saboda dalilai na siyasa da bangarancin banbancin mazhaba.
(last modified 2018-08-22T11:28:43+00:00 )
Aug 07, 2016 05:23 UTC
  • Masarautar Bahrain Ta Kame Manyan Malamai Uku Na Kasar

Masarautar mulkin mulukiya ta kasar Bahrain ta kame manyan malaman addini na kasar guda uku saboda dalilai na siyasa da bangarancin banbancin mazhaba.

Tashar talabijin ta Alalam ta bayar da rahoton cewa, daga cikin malaman da aka kama har sheikh Muhsin Alguraifi, da sheikh Fadil Zaki, da kuma sheikh Ali Naji Almuhli.

Wannan mataki yana zuwa ne a daidai lokacin da masarautar mulkin kama karya ta kasar Bahrain ke ci gaba da yunkurin ganin cewa bisa dalilai na siyasa da kuma banbancin mazhaba ta mayar da mabiya mazhabar shi’a na kasar saniyar ware a cikin dukkanin lamurra kasar.

Kafin wannan lokacin dai masarautar ta kame Sayyid majid Masha’al shugaban majalisar malaman addinin muslunci ta kasar, bisa hujjar cewa yana goyon babban malamin addini na kasar wanda baya dasawa da wannan masarauta.

A cikin shekara ta 2014 ce masarautar ta sanar da soke majalisar malaman addini ta kasar kasantuwar cewa akasarinsu mabiya mazhabar shi’a ne, ba tare da yin la’akari da cewa fiye da kashi tamanin biyar cikin dari na mutanen kasar mabiya mazhabar shi’a ne ba.