Christine Lagarde Ta Sake Zama Shugabar Asusun IMF
Feb 19, 2016 13:35 UTC
Mme Lagarde zata sake shugabancin asusun a wani wa'adi na shekaru 5.
Kasashe membobin asusun bada lamuni na duniya wato IMF ko kuma FMI sun sake baiwa Christine Lagarde damar shugabancin hukumar.
hakan dai na nufin Mme Lagarde 'yar asalin kasar Faransa zata sake shugabancin asusun a wani sabon wa'adi na shekaru biyar.
Mme Lagarde dai 'yar shekaru 60 a duniya wace ita kadai ce 'yar takara a neman shugabancin asusun na IMF za ta fara aiki a sabon wa'adin nata a watan Yuli mai zuwa.
Lagarde, ta fara jagorancin asusun IMF ne a shakara 2011, bayan maye gurbin Dominique Strauss-Kahn daya sinci kan sa cikin badakalar rashawa a Sofitel na New york.
Tags