Azhar: Ta'addanci Kaucewa Koyarwar Addinin Musulunci Ne.
https://parstoday.ir/ha/news/world-i10172-azhar_ta'addanci_kaucewa_koyarwar_addinin_musulunci_ne.
Kaucewa Koyarwar Musulunci Ya ke jawo aikata ta'addanci
(last modified 2018-08-22T06:58:49+00:00 )
Aug 26, 2016 07:19 UTC
  • Azhar: Ta'addanci Kaucewa Koyarwar Addinin Musulunci Ne.

Kaucewa Koyarwar Musulunci Ya ke jawo aikata ta'addanci

An bayyana cewa gurbatacciyar fahimtar da wasu su ka yi wa addinin musulunci ya sa su ke fakewa da sunansa suna aikata ta'addanci.

Shugaban Jami'ar Azhar ta Masar, Sheik Ahmad Tayyib ya fada a jiya alhamis cewa; Musulunci ya zo ne domin ya samar da 'yanci da kuma  kare jinanen mutane da kiyaye su.

Shugaban na Azhar da ya gana da shugaban jami'ar musulunci ta Cheheniya  Abdurrahim Motoshiv ya kara da cewa  Hanya guda ta ficewa daga cikin wannan yanayin da ake ciki na ta'addanci shi ne komawa zuwa ingantacciyar koyarwar addinin musulunci.