Ministan Cikin Gidan Faransa: Haramta Burkini Ya Saba Kundin Tsarin Faransa
https://parstoday.ir/ha/news/world-i10336-ministan_cikin_gidan_faransa_haramta_burkini_ya_saba_kundin_tsarin_faransa
Ministan cikin gidan kasar Faransa Bernard Cazeneuve ya bayyana cewar haramta wa mata sanya tufafin ninkaya da ke rufe dukkanin jiki da ake kira da burkini ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar wanda kuma ba abin da zai janyo in ba da tashin hankali da husuma tsakanin 'yan kasar.
(last modified 2018-08-22T06:58:51+00:00 )
Aug 30, 2016 01:25 UTC
  • Ministan Cikin Gidan Faransa: Haramta Burkini Ya Saba Kundin Tsarin Faransa

Ministan cikin gidan kasar Faransa Bernard Cazeneuve ya bayyana cewar haramta wa mata sanya tufafin ninkaya da ke rufe dukkanin jiki da ake kira da burkini ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar wanda kuma ba abin da zai janyo in ba da tashin hankali da husuma tsakanin 'yan kasar.

Jaridun kasar Faransan sun jiyo ministan cikin gidan Bernard Cazeneuve yana fadin cewa duk da cewa wasu daga cikin 'yan siyasar kasar sun yi na'am da haramta burkini din amma dai to amma gwamnatin Faransa dai tana nesanta kanta daga hakan don kuwa irin wannan dokar  ta saba wa kundin tsarin mulkin kasar, kuma ta da wani amfani kana kuma za ta taimaka ne wajen haifar da rikici da kace nace.

Ministan cikin gidan ya kara da cewa a halin yanzu kasar Faransa tana bukatar kyautata mu'amalarta da musulmi, to sai dai su ma musulmin akwai bukatar su yi taka tsantsan.

Batun Burkini dai ya janyo muhawara mai zafi a kasar Faransan tun bayan wasu hotunan da aka yada na wasu ‘yan sanda suna tilasta wa wata mata cire tufafinta da ta rufe jikinta a gabar tekun.

Wannan dai na zuwa ne bayan da wata kotu ta dakatar da dokar haramcin Burkini, duk kuwa da wasu magajunan gari a Faransan sun ce za su bijirewa wannan dokar.