Damuwar Holland kan takunkumin da aka kakabawa Rasha
https://parstoday.ir/ha/news/world-i10372-damuwar_holland_kan_takunkumin_da_aka_kakabawa_rasha
Shugaban Kasar Faransa ya bayyana damuwarsa kan takunkumin da aka kakabawa kasar Rasha
(last modified 2018-08-22T06:58:51+00:00 )
Aug 31, 2016 03:26 UTC
  • Damuwar Holland kan takunkumin da aka kakabawa Rasha

Shugaban Kasar Faransa ya bayyana damuwarsa kan takunkumin da aka kakabawa kasar Rasha

A yayin da yake jawabin shekara shekara na Ma'aikatar harakokin wajen kasarsa a jiya Talata, Shugaba Holland na kasar Faransa ya bayyana cewa takunkumin da Kungiyar tarayyar Turai ta kakabawa kasar Rasha abin takaici ne kuma zai cutar da dukkanin bangarorin biyu, hasali ma zai dakatar da manya manyan aiyuka da bangarorin suka gudiri aikatawa,

Shugaba Holland ya bayyana fatansa na ganin an samu canji a wannan bangare, kafin hakan dai, Majalisar dokokin kasar ta bukaci da a dage takunkumin da aka kakabawa kasar Rasha, ita ma Majalisar Datijan kasar ta zartar da wata doka inda ta bukaci a sassauta takunkumin da aka kakabawa Rasha.

A cikin shekaru biyu na baya bayan nan alakar dake tsakanin Rasha da Kungiyar Tarayyar Turai da kuma Kungiyar Nato ta yi tsami sakamakon rikicin kasar Ukrene.

Domin goyon bayan Amurka, Kungiyar Tarayyar Turan ta kakabawa Rasha takunkumin tattalin arziki da kuma sanya wasu magabatan Rashan a jarin sunayen da aka kakabawa wannan takunkumi.