Taimakon Faransa ga kasashen Afirka
Kasar Faransa ta yi alkawarin kara taimakon da ta ke baiwa wasu Kasashen Afirka a bangaren tsaro.
A yayin da yake ziyarar aiki a kasar Burkina Faso,Firaministan Kasar Faransa Manuel Valls ya ce Gwamnatinsa za ta kara yawan taimakon bangaren tsaro da take baiwa kasar Burkina da ma sauren kasashen yankin sahel domin yaki da ta'addanci.
Bayan sama da wata guda da kai harin ta'addancin a kasar burkina Faso, a jiya Assabar Firaministan Faransa Manuel Valls ya isa birnin Ouagadougou domin jajantawa shugaban kasar Roch Marc Christian Kaboré da Al'ummar kasar
A ranar 15 ga watan Janairun da ya gabata ne 'yan kungiyar Murabutun mai alaka da kungiyar Alka'ida suka kai wani mumunan hari ta'adanci a wata babbar Otel da wani gurin cin abinci dake Ouagadugu babban birnin kasar Burkina Faso, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 30 tare kuma da jikkatar wasu 70 na daban.
A cewar kamfanin dillancin Labaran Reuteus, kafin ya isa kasar Burkina Faso, Firaministan kasar Faransan sai da ya yada zango a kasar Mali, inda ya gana da shugaban kasar Ibrahim Boubacar Kieta har so biyu,bayan tattaunawarsu ya shaidawa manena Labarai cewa wajibi ne kasarsa ta karfafa horon da take bayarwa ga dakarun kasasashen Afirka da kuma bangaren masayar bayanai.
Kasar Faransa dai ita ce kasa mafi girma da take yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda a yankin Sahel inda yanzu haka ke da Sojoji dubu 350 a yankin.