Shugabannin EU sun amince da sabon tsari
Taron kolin EU ya amince da wata sabuwar fuska ci gaba
Shugabannin kasashen kungiyar tarayyar Turai 27 a karshen taron kolin da suka gudanar a Bratislava babban birnin kasar Slovakia sun amince da sabon tsari da zai ciyar da kungiyar gaba na tsahon watani shida ba tare da halartar Theresa May sabon Piraministan Birtaniya ba
sabon tsarin dai ya kunshi hanyoyi da kuma dabarun inganta amincin al'umma da kuma yarda a tsakanin kasashen kungiyar bayan sakamakon ba zata na kuri'ar raba gardamar da Birtaniya ta kada na ficewa daga cikin kungiyar.
Mahalarta taron sun ce an gudanar da tattaunawar cikin nasara.kuma dukkanin kasashen 27 sun jaddada kudirin su na yaki da ta'addanci domin tabbatar da tsaron nahiyar ta Turai.
A karshen taron Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da Francois Holland Shugaban kasar Faransa sun tabbatar da cewa Kasashen su za su iya kokarin su wajen ganin an zartar da yarjejjeniyar tun daga wata mai kamawa kuma kada yi tsammanin a taro guda za'a warware dukkan matsalolin da nahiyar Turai ke fuskanta.sannan kuma sun shakka babu muna cikin wani yanayi na tsaka mai wuya, to amma wannan dama ce ta nuna cewa ta hanyar daukar mataki, za mu iya inganta lamura musamman ta fuskar tsaro a cikin gida da waje da kuma yaki da ta'addanci."