Bikin Edul-Ghadir A Tsakanin Mabiya Ahlul-Bayt (a.s)
(last modified Tue, 20 Sep 2016 06:22:58 GMT )
Sep 20, 2016 06:22 UTC
  • Bikin Edul-Ghadir A Tsakanin Mabiya Ahlul-Bayt (a.s)

A yau ake raya edul-ghadir a duniyar musulmi

Mabiya ahlul-Bayt ( a.s) suna raya ranar Ghadir da manzon Allah (s.a.w.a ) ya annaya Imam Ali (a.s) a matsayin magajinsa.

A cikin Iraki mabiya mazhabar ahlul-Bayti (a.s) sun taru a hubbaren Imam Ali (a.s) da ke birnin Najf inda  su ke murnar zagayowar wanann rana ta Ghadir.

A hubbaren Sayyida Zainab (salamullahi Alaiha)  da ke birnin Damascuss na kasar syria 'yan shi'a sun taro a daren jiya domin raya wannan rana.

Bikin Ranar Ghadir ya samo asali ne daga ranar 18 ga watan Zulhijja na shekarar hijira ta 10 da ma'aikin Allah (s.a.w.a ) ya fadawa taron musulmin da su ke barin makka domin kowawa madina daga aikin haji a wani wuri da ake kira; Ghadir Khum, cewa; Duk wanda na kasance jagoransa, to Ali ma jagoransa ne."

A madadin sashen Hausa na muryar jamhuriyar musulunci ta Iran da ma'aikatansa, suna taya dukkanin muminai murnar zagayowar wannan rana.