Kasar Faransa Zata Rufe Wani Sansanin Yan Gudun Hijira A Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/world-i11380-kasar_faransa_zata_rufe_wani_sansanin_yan_gudun_hijira_a_kasar
Ministan harkokin cikin gida na kasar Faransa ya bayyana cewa gwamnatinsa zata rufe wani sansanin yan gudun hijira da ke Kole .
(last modified 2018-08-22T06:58:58+00:00 )
Sep 22, 2016 04:13 UTC
  • Kasar Faransa Zata Rufe Wani Sansanin Yan Gudun Hijira A Kasar

Ministan harkokin cikin gida na kasar Faransa ya bayyana cewa gwamnatinsa zata rufe wani sansanin yan gudun hijira da ke Kole .

Jaridar Le figaro ta kasar Faransa ta nakalto Bernard Cazeneuve yana fadar haka a jiya Laraba ya kuma kara da cewa an bude sansanin yan gudun hijira na Kole ne a cikin watan Octoba na shekara ta 2015, kuma a halin yanzu gwamnati zata rufe sansanin sannan ta rarraba yan gudun hijira na wannan sannin zuwa wasu yankuna na kasar faransa. Ministan ya ce hakan zai bawa gwamnatin kasar faransa sanya ido a kan dukkan yan gudun hjira da kuma basu cikekken mafaka a kasar.

Wannan matakin da gwamnatin kasar faransa ta dauka dai ya fusata wasu shuwagabannin lardunan kasar wadanda suka ce ba'a shawarce su kan lamarin ba, kuma wannan matakin da gwamnatin ta dauka bai yi dai dai ba. A ranar laraban da ta gabata ce yan gudun hijiran da suke zaune a sansanin suka yi kokarin ficewa daga sansanin don isa kasar Britania amma yansanda sun hana su yin hakan tare da tarwatsa su da hayaki mai sa hawaye.