Kashe Wata Mace Mai Sanye Da Hijibi A Kasar Faransa
https://parstoday.ir/ha/news/world-i11551-kashe_wata_mace_mai_sanye_da_hijibi_a_kasar_faransa
Wani dan bindiga ya kashe wata mace mai sanye da hijibi a garin Pantin na kasar Faransa.
(last modified 2018-08-22T06:58:59+00:00 )
Sep 25, 2016 07:47 UTC
  • Kashe Wata Mace Mai Sanye Da Hijibi A Kasar Faransa

Wani dan bindiga ya kashe wata mace mai sanye da hijibi a garin Pantin na kasar Faransa.

Kafar watsa labaran Faransa ta bayyana cewa: Wani dan bindiga ya harbe wata mace musulma 'yan asalin nahiyar Afrika har lahira a lokacin da take tukin motarta a garin Pantin Ile-de -France a gundumar Seine-Saint -Denis na kasar Faransa a cikin daren Juma'a.

Kafar watsa labaran ta Faransa ta kara cewa: Harbi biyu ya yi mata a kai, sannan makashin ya tsere, sai dai majiyar 'yan sandan garin ta yi da'awar cewa: Kisan gillar baya da alaka da nuna kiyayya ga addinin Musulunci, iyaka dai akwai wata matsala da ke tsakanin mutane biyu amma ana ci gaba da gudanar da bincike don gano makashin.