EU Ta Cire FARC Daga Jerin Kungoyoyin 'Yan Ta'adda
Kungiyar tarayya turai ta cire kungiyar 'yan tawayen FARC ta Columbiya daga cikin jerin kungiyoyin 'yan ta'adda bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar kawo karshen yakin basasar kasar.
Wata sanarwa da kwamitin shawara na kungiyar ya fitar Jiya Litinin ta ce an dakatar da kudiri na EU akan kungiyar 'yan tawayen na FARC.
Wani jami'in kungiyar ya shaidawa manema labarai cewa bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar zamen lafiya da bangarorin biyu suka cimma an cire kungiyar ta FARC daga jerin kungoyoyin 'yan ta'adda.
Tun a shekara 2002 ne kungiyar EU ta sanya sunayen wasu jagororin kungiyar ta FARC cikin jerin kungiyoyin 'yan ta'adda.
A jiya ne dai shugaban kasar Colombia Juan Manuel Santos ya sanya hannu kan yarjejeniyar kawo karshen yakin basasar kasar da shugaban kungiyar 'yan tawayen FARC, Timoleon ‘Timochenko’ Jimenez.