Siriya : EU Ta Kaddamar da Shirin Agajin Gaggawa A Halep
kwamitin tarayya Turai ya sanar da kaddamar da wani shirin agajin gaggawa na kungiyar ta (EU) domin baiwa kungiyoyin agaji damar taimakawa al'ummar Halep dake cikin tsaka mai wuya a daidai lokacin ake ci gaba barin wuta ta sama da kasa a yankin.
Kungiyar ta EU ta ce zata samar da kudade da yawansu ya kai milyan 25 na Yiro (Euro) ga kungoyoyin agaji abokan huldarta domin samar da magunguna, isar da ruwan sha da abinci a Halep.
Babbar jami'ar diflomatsiya ta kungiyar ce Frederica Mogherini, da kwamishinan kula da harkokin jin kai na kungiyar Christos Stylianides suka sanar da hakan yau Lahadi.
kungiyar ta EU dai ta ce ta dau wannan matakin ne hadin gwiwa da MDD domin tunkara bala'in dake ci gaba da faruwa a Halep, tare da kira ga dukkan bangarorin da rikicin ya shafa su taimaka mata don cimma wannan gurin.
Kungiyar dai ta ce tana fatan soma wannan aikin cikin gajeren lokaci.