Shugaban Kasar Bolivia ya kasa samun nasara
(last modified Wed, 24 Feb 2016 09:21:37 GMT )
Feb 24, 2016 09:21 UTC
  • Shugaban Kasar Bolivia ya kasa samun nasara

Shugaba Evo Morales bai samu nasara ba a kuri'ar sauraron ra'ayin jama'a

Kamfanin Dillancin Labarun Reuters ya ambato cewa; Shugaban kasar bolivia Evo Morales ya sha kashi a kuri'ar sauraron jama'a dangane da ko zai iya sauya kundin tsarin mulki domin yin tazarce.

Da safiyar yau alhamis ne hukumar zaben kasar ta Bolivia ta sanar da sakamakon kuri'ar sauraron ra'ayin jama'ar da aka yi wanda ya nuna cewa, al'ummar kasar ba su amincewa wa Morales ya yi tazarce ba, bayan da ya yi zango na uku yana mulki.

Morales wanda shi ne dan asalin kasar na farko da ya zama shugaban kasa a 2006 yana da magoya baya da su ke jinjina masa saboda fada da talauci da ya yi, sai dia a lokaci guda yana fuskantar suka saboda cin hanci da rashawa a cikin jam'iyyarsa.

A shekarar 2019 ne za a sake yin zabe a kasar ta Bolivia