Mahaukaciyar Guguwar 'Mathew' Ta Hallaka Mutane 23 A Kasar Haiti
(last modified Thu, 06 Oct 2016 10:57:29 GMT )
Oct 06, 2016 10:57 UTC
  • Mahaukaciyar Guguwar 'Mathew' Ta Hallaka Mutane 23 A Kasar Haiti

Mahaukaciyar guguwa da ta haifar da ambaliyar ruwa da aka ba wa suna "Matthew" ta kashe mutane 27 a kasar Haiti da Jamhuriyar Dominican yayin da mutanen kuma sun bace babu labarinsu.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa daga birnin Port-au-Prince, babban birnin kasar Haitin sun bayyana cewar alal akalla mutane 23 sun mutu a kasar Haiti kana wasu 4 kuma sun mutu a kasar jamhuriyar Dominican sakamakon wannan mahaukaciyar guguwar wacce kuma ta nufi kasashen makwabta. 

Hukumomi a kasar Haiti sun ce hanyoyin sadarwa sun katse a kudancin kasar saboda yadda guguwar dake dauke da ruwa ta lalata turakan sadarwa, da kuma rusa gadar da ta hada Port-au-Prince din da tsibirin Haiti, kamar yadda suka ce mutane suna  cikin mawuyacin hali sakamakon wannan guguwar lamarin da ya  sanya ake tsoron sake bulluwar wasu cututtuka a kasar.

Rahotanni sun ce guguwar wacce  ita ce mafi muni a tsawon shekaru kusan goman da suka ce a yankin tana gudun kilomita 220 a cikin sa’a guda.