Adawar Faransa kan sake kakabawa Rasha takunkumi
Gwamnatin Faransa ta nuna rashin amincewar kan sake kakabawa Rasha takunkumi saboda rikicin kasar Siriya
Jaridar Le Pigaro ta kasar Faransa ta nakalto Ministan harakokin wajen kasar faransa Jean-Marc Ayrault cikin wani taron manema labarai da ya gabatar a birnin Rom na kasar Italiya jiya Laraba, yayin da yake magana kan rikicin kasar Siriya ya ce duk da kiraye kirayen da aminan su ke yi na kakabawa Rasha takunkumi cikin gaggauwa ,kasar Faransa ba za ta goyi bayan hakan ba,
Mainistan ya bayyana hakan ne bayan da ya gana da takwarorinsa na kasashen Italiya da Jamus, inda ya ce duk da cewa abin da ke faruwa a kasar Siriya musamman ma a yankin Allepo ba abin da za a jurewa ba ne to amma daukan matakin takunkumi ba ya gaban Faransa a yanzu.
Kasashen Faransa da Rasha na da sabani mai tsanani dangane da rikicin Siriya inda ko wannan su ke zarkin dan uwan sa da rura wutar rikicin.