MDD za ta baiwa Al'ummar Zirin Gaza diya
https://parstoday.ir/ha/news/world-i12922-mdd_za_ta_baiwa_al'ummar_zirin_gaza_diya
Ofishin dake kula da shirin bunkasa na MDD ya sanar da cewa Iyalai 1339 ne na Al'ummar yankin Palastinu da yakin 2014 ya yi sanadiyar rusa gidajensu za a biya su diya.
(last modified 2018-08-22T11:29:08+00:00 )
Oct 25, 2016 05:46 UTC
  • MDD za ta baiwa Al'ummar Zirin Gaza diya

Ofishin dake kula da shirin bunkasa na MDD ya sanar da cewa Iyalai 1339 ne na Al'ummar yankin Palastinu da yakin 2014 ya yi sanadiyar rusa gidajensu za a biya su diya.

Kamfanin dillancin Labaran Isna ya nakalto Ofishin dake kusa da shirin Bunkasa na MDD na cewa an ware kudi na musamman domin taimakawa iyalan da suka rasa gidajen su ko kuma wani bangare na gidajensu ya rushe ta yadda ba zai yiyu su iya ci gaba da rayuwa a cikin sa ba na yankin Zirin Gaza. kudin da aka ware domin taimakawa wadannan iyalai, dalar Amurka Miliyan guda da dubu 547 da 600.

A ranar 7 ga watan yunin shekarar 2014, Haramcecciyar kasar Isra'ila ta fara yakar Al'ummar yankin zirin Gaza na Palastinu, lamarin da yayi sanadiyar shahadar Palastinawa 2320, tare kuma da rusa gidaje dubu 12 gaba daya da kuma wani bangare da gidaje dubu 16 daga cikin su a kwai 6600 da babu yadda za a iya rayuwa a cikin su ba.