Shahadar Bapalasdine Daya A Yammacin Kogin Jordan
https://parstoday.ir/ha/news/world-i13351-shahadar_bapalasdine_daya_a_yammacin_kogin_jordan
Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra'ila Sun Kashe Bapalasdine daya a yau alhamis.
(last modified 2018-08-22T06:59:11+00:00 )
Nov 03, 2016 14:34 UTC
  • Shahadar Bapalasdine Daya A Yammacin Kogin Jordan

Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra'ila Sun Kashe Bapalasdine daya a yau alhamis.

Kamfanin Dillancin Labarun ( AFP) ya nakalto majiyar sojojin haramtacciyar Kasar Isra'ila na cewa; sun harbe wani bapalasdine bayan da ya yi kokarin sukar sojan nasu da wuka.

Bayanin sojojin yahudawan sahayoniyar ya ci gaba da cewa; Sojojin Sun harbe Bapalasdi nan ne a  kusa da tashar motar Bus ta Ofra, inda nan take ya mutu.

Majiyar ma'aikatar lafiya ta palasdinawa kuwa ta bayyana cewa; Sarayin da yan sahayoniyar su ka harbe mai suna Mu'in Nasiruddin Abu Qarr, shekarunsa 23 kuma ya fito ne daga kauyen mazra'al qabaliyyah a kusa da birnin Ramallah.

Daga watan Oktoba na shekarar 2015 da ta gabata zuwa yanzu, palasdinawa 238 nesu ka yi shahada a bisa kididdigar kamfanin dillancin labarun Faransa.