Amurka Ta Yarda Cewa Ta Kashe Fararen Hula A Afganistan
Rundinar sojin Amurka ta yarda cewa harin data kai a Afganistan mai yiwa shi ne ya kashe fararen hula a lardin Kunduz inda fararen hula akalla 30 suka rasa rayukansu.
Wannan dai na zuwa ne bayan da shugaban kasar ta Afganistan ya aike da wata tawaga ta musamen a Kundiz domin binciken abunda ya faru.
kakakin gwamnatin yankin Haroon Chakhansuri ya shaidawa masu aiko da rahotanni cewa ba za'a rufe ido akan wannan sakaci ba, domin za'a dauki mataki akai.
Shi ma nasa banagre Janar Charles Cleveland daya daga cikin kwamandodin Amurka a kasar ta Afganistan ya ce za'a gudanar da bincike kan lamarin tare da hadin gwiwa da rundinar sojin kasar ta Afganistan.
Kafin hakan dai an rawaito cewa kawacen dakarun kasashen biyu dake sintiri a yankin na Kunduz ya fuskanci hare hare daga wasu tsageru, lamarin daya sa ya bukaci taimakon harin jiragen sama na Amurka.