Shafin Donald Trump Ya Cire Wasu Kalaman Batunci Kan Musulmi
https://parstoday.ir/ha/news/world-i13696-shafin_donald_trump_ya_cire_wasu_kalaman_batunci_kan_musulmi
Masu kula da shafin yanar gizo na Donald Trump zabebben shugaban kasar Amurka sun cire irin kalaman batuncin da ya rika yi a kan musulmi daga shafin nasa.
(last modified 2018-08-22T06:59:13+00:00 )
Nov 10, 2016 12:10 UTC
  • Shafin Donald Trump Ya  Cire Wasu Kalaman Batunci Kan Musulmi

Masu kula da shafin yanar gizo na Donald Trump zabebben shugaban kasar Amurka sun cire irin kalaman batuncin da ya rika yi a kan musulmi daga shafin nasa.

Kamfanin dillancin labaran express cewa, baya ga cire kalaman batunci kan musulmi daga shafin Trump, a lokacin jawabinsa na farko bayan samun nasara, ya bayyana cewa za su yi aiki tare da kowa ba tare da nuna kyama ga wani ba.

Donald Trump ya kara da cewa, duk da cewa maslahar Amurka ita ce a gaba a kan komai a wurinsa, amma kuma zai yi mu'amala tare da dukkanin kasashe na duniya bisa mutunci da girmama juna.

Kamar yadda ya ce kuma zai hada da kai tare da dukkanin mutanen Amurka ba tare da nuna banbanci na addini ko siyasa ko kabilanci ba, sabanin kalaman da aka saba ji daga bakinsa a lokutan baya.

A cikin watan Disamban shekarar 2015 da ta gabata ce, Trump ya bukaci da a hana musulmi shiga cikin kasar Amurka, tare da yin kira da a rika sanya ido a kan sauran musulmin da ke cikin kasar, tare da bincika masallatansu da wuraren ibadarsu.