Yemen : Gwamnati Mai Murabus Tayi Watsi Da Tayin John Kerry
Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry ya sanar da wani sabon shirin samar da zamen lafiya a kasar Yemen, saidai tun ba'a kai ko ina ba gwamnatin Abdul Rabo Mansur Hadi mai murabus dake samun goyan bayan Saudiyya tayi watsi da wannan shirin.
Shirin dai ya tanadi tsagaita wuta daga ranar Alhamis mai zuwa da kuma kafa gwamnatin hadin kan kasa kafin karshen wannan shekara.
Da yake bayyana hakan gaban manema labarai a birnin Abu Dabi, Mista Kerry ya ce 'yan gwagwarmar neman sauyi na Houthis sun ce sunyi maraba da shirin na tsagaita wuta muddun dai sauren bangarorin zasu mutunta shi.
Mr Kerry ya ce ya samu tattaunawa ta kud da kud da wakilan 'yan Houtsis da suka kai masa ziyasa ta musamen a Oman inda ya yada zango a Jiya Litinin kuma sun fada masa kyakyawan fatran su na ganin an kawo karshen rikicin daya daidaita kasar ta Yemen.
Kuma a karshen ganawar sun fitar da wani gajeren tsari da zai taimaka wajen ciyar da tattaunawar samar da zamen lafiya a kasar a gaba, lamarin daya sa sakateren harkokin wajen na Amurka ya tattauna da mayan jami'an kasar Saudiyya da hadaddiyar daular Larabawa dake jagorancin farmakin zaluncin da ake ci gaba da kaiwa al'ummar kasar ta Yemen.