Rikici Ya Kunno Kai Cikin Kwamitin Karbar Mulki Na Donald Trump
Rahotanni daga Amurka suna nuni da cewa tun ba a je ko ina ba an fara samun baraka cikin kwamitin karbar mulki da zababben shugaban kasar Amurka Donald Trump ya kafa inda wasu daga cikin kusoshin tawagar suka fara yin murabus sannan kuma ake ta kace nace dangane da irin rawar da iyalansa Mr. Trump din za su taka a wannan fagen.
Rahotanni sun bayyana cewar babban mai ba wa Mr. Trump din shawara kan harkokin tsaro Mike Rogers ya sanar da ficewarsa daga kwamitin karbar mulkin ne a wani abu da ake ganinsa a matsayin ci gaba da rikicin da ke faruwa a cikin tawagar karbar mulki.
Gwamnan jihar New Jersey Chris Christie kuma daya daga cikin na kurkusa da Mr. Trump din ne ya fara sanar da murabus dinsa a matsayin shugaban kwamitin karbar mulki lamarin da ya share fagen ficewar wasu daga cikin tawagar musamman ma a bangaren tsaron kasa. Murabus din gwamna Chris Christie yana nuni da gagarumin sabani da rarrabuwar kan da ta kunno kai a cikin tawagar ta Mr. Trump.
Har ila yau kuma wasu rahotannin suna cewa akwai wani rikicin ma da ya barke a cikin tawagar Mr. Trump dangane da rawar da wasu daga cikin 'ya'yansa da kuma danginsa za su taka a kwamitin karbar mulkin.
Ana ganin bullowar wannan rikicin dai zai cutar da kokarin saboda shugaban na kafa wata tsayayyiyar gwamnati a Amurkan