An Murkushe Yunkurin Kai Sabon Harin Ta'addanci A Faransa
Hukumomi a kasar Faransa sun sanar da cafke mutane bakwai wadanda ake zargi da yunkurin kai wani sabon harin ta'addanci a kasar.
Mutanen da aka cafke 'yan tsakanin shekara 29 zuwa 37, sun hada da 'yan asalin kasar ta Faransa da Marocco da kuma Afganistan, kuma dukkansu an cafke su a yankin Strasbourg da Marseille, bayan shafe watanni takwas da bude wani binkicen ta'addanci.
An dai murkushe yunkurin kai harin da aka dade ana shiryawa ne a karshen makon jiya, kamar yadda ministan cikin gida na kasar, Bernard Cazeneuve, ya sanar a wannan Litinin.
Ministan ya kara da cewa za'a binciki mutanen domin sanin ko jerin hare hare ne suke shirin kaiwa ko kuma A'a.
Faransa dai ta jima tana fuskantar hare hare ta'addanci, mafi muni a cikin su kuwa sun hada da wadanda aka kai a watan Nuwamba bara a wasu wuraren shakatawa dake Paris babban birnin aksar inda mutane 130 suka hallaka, sai kuma wanda aka kai a watan Yuli na wannan shekara a birnin Nice inda mutane 86 suka mutu.