Indiya : Mutane 146 Suka Mutu A Hadarin Jirgin Kasa
(last modified Mon, 21 Nov 2016 16:18:24 GMT )
Nov 21, 2016 16:18 UTC
  • Indiya : Mutane 146 Suka Mutu A Hadarin Jirgin Kasa

Ma’aikatan agaji a kasar Indiya sun sanar da kawo karshen aikin lalabo masu sauran kwana a mummunan hatsarin jirgin kasa da ya auku a jihar Uttar Predash kusa da garin Kanpur a arewacin kasar.

Kawo yanzu dai mutane 146 aka tabbatar da mutuwarsu sanadin hatsarin inda 145 suka mutu nan take yayin da guda ya cika a asibiti kamar yadda kakakin kanfanin jirgin kasa na kasar, Vijay Kumar ya sanar ga manema labarai a wannan Litinin.

Hakazalika a cewar Mr Kumar, akwai wasu mutane 180 dake jinya a asibiti wadanda kuma suka hada da 60 da suka ji munanen raunuka. 

Binciken farko farko dai ya nuna cewa jirgin ya jirkice ne saboda matsalar daya daga cikin layin dogo.

A halin da ake ciki dai a cewarsa an kwashe na'urorin da aka jibge don gudanar da aikin ceto, kuma ana sa ran cikin daren nan zuwa Talata a fara zurga-zurga jiragen kasa a yankin.

Wannan shi ne hatsari mafi muni a kasar tun hatsarin wani jirgin kasa a shekara 2010 inda mutane 146 suka mutu tare da jikkata sama 200.